Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Har ila yau sojojin Isra’ila suk kutsa kai kauyen al- Zaeem dake gabashin birnin Kudus tare da lalata musu filayen noma, haka ma a kauyen Isawiya dake Arewacin birnin Kudus dakarun na Isra’ila sun lallata amfanin gonan falasdinawa ,
Hukumomi kasa da kasa na daukar ci gaba da gine gine da Isra’ila take yi a yankunan falasdinawa da ta mamaye a matsayin take dokokin kasa da kasa, kuma babban cikas a kokarin da aka yi na kafa kasashe biyu masu cin gashin kai da zai warware rikicin dake tsakanin bangarorin biyu.
Kimanin yahudawa 700,000 ne ke rayuwa a matsugunnan yahudawa da Isra’ila ta gina a yankunan da ta mamaye tun a shekara ta 1967 a gabar yammacin kogin jodan da kuma Gabashin birnin Qudus.
342/